Ambaliyar Ruwa: Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar da Rabon Kayan Tallafi Read more

Gwamnan jihar Jigawa, Mai girma Umar Namadi ya waiwayi mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a daminar na.

Gwamnan ya amince a fitar da N315.5m domin rabawa ga mutane 15,775 da ke a sansanonin ƴan gudun hijira a inda lamarin ya shafa.

Namadi ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da tallafi ga mutanen tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.

Gwamna Namadi ya ba da tallafin ambaliya

Gwamnan wanda ya je ƙaddamar da rabon kayayyakin tallafi ga mutanen ya bayyana cewa za a ba da tallafin kuɗin ne da abinci domin rage raɗaɗin da suka fuskanta sakamakon ambaliyar ruwan, rahoton Leadership ya tabbatar. Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa gwamnatinsa ta damu da mutanen da lamarin ya shafa tun farkon faruwar ambaliyar ruwan kuma za ta ci gaba da ba su tallafi tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.

0 Shares

Leave a Reply