Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Zai Ziyarci Kasar Faransa A Yau (DUBI BAYANI)

   An kammala shirye-shiryen shugaban kasa Bola Tinubu zai tafi kasar Faransa ranar Litinin.

Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a daren Lahadi, ta bayyana cewa shugaban zai tashi ne daga Abuja, babban birnin kasar.

Ngelale ya bayyana cewa shugaban zai koma kasar ne bayan gajeriyar aikinsa a Faransa.

Sai dai sanarwar ta yi shiru ne kan dalilin tafiyar shugaban.

 

Shugaban ya hana jami’an gwamnati da ba su izini ba halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, UNGA da za a yi a birnin New York na Amurka.

Fadar shugaban kasar dai ta dora wannan umarni ne a kan bukatar rage yawan kuɗaɗen gudanar da mulki, musamman yadda jami’an da ba su da izini a baya suka yi tafiye-tafiyen don biyan bukatun kansu.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajiabiamila ne ya mika wa jami’an gwamnati wannan umarni a yayin wani taron kwana daya da mahukuntan fadar gwamnati suka shirya wa shugabannin hukumomin da ke karkashin fadar shugaban kasa.

0 Shares

Leave a ReplyCancel reply